Ya kamata shugabanni su ji tsoron Allah su tuna za'a tambaye su yadda suka gudanar da mulki ranar tashin alkiyama.
Kuma akwai wata addu'a da Manzon Allah yayi mai zafi game da shugabanni: ((ya daga hannu a dakin Ummuna A'isha, yace: ya Ubangiji dukkan wanda ya jibinci al'amarin al'ummata ya shugabance su in yayi musu sauki sunji dadin gudanar da mulkinsa bai zalunce su ba, ya Ubangiji ka saukaka masa, ka saukaka masa, ka saukaka masa.
Sannan kuma yace: ya Ubangiji dukkan wanda ya shugabanci al'ummata kuma ya jefa su cikin 'kunci cikin halin 'ka'kani-kayi, yace: ya Ubangiji ka 'kuntata masa, ka 'kuntata masa, ka 'kuntata masa)).
Kaga wannan addu'a mai tsanani Manzon Allah ya riga yayi ta ga shugabanni, dan haka wannan sai ya zama wajibi ga dukkan wanda yake shugaba wanda yake shugabantar jama'a ya sani cewa ga addu'ar Manzon Allah a kansa.
Kuma Manzon Allah dai yace: ((kullukum ra'in wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi))".
Allah ya zaba mana Shugabanni na Kwarai a wannan kasa tamu mai albarka. Amin.
Wannan Sako ne daga Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa Iqamatis Sunnah ta kasa.
UNDER MAINTENANCE