Hakika a cikin irin wannan matsalar malammai sun yi bayanai daban~daban, wasu malaman sunce:duk mutumen da ya kyautatawa mahifinasa, to shima lallai 'ya'yansa zasu kyautata masa idan kuma yayi wa mahaifansa rashin mutunci..nasa 'ya'ya zasu yi masa rashin mutunci kamar dai yanda yazo a hadisi
Wasu malaman sunkace babu babban dalilin da yake sa 'ya'ya su zama marassa kirki shine rashin kula da hakkinsu
Wasu malaman sukace a'a matukar dai uba zai nemo haram ya kawo a gidan sa to tabbas shi kuma zai ci karo da matsalar rashin kyautatawa ga 'ya'yansa..
Wasu malaman sunkace a'a ai tushen lalacewa ''ya'ya shine rashin uwa ta gari.
wasu malaman kuwa ganin suke rashin ladabin 'ya'ya ya ta allakane daga rashin sanaddasu ilimin Addini,,domin duk mutumen da bashi da ilimi lailai ne ya zama mai wauta ga jima a domin baisan hakkinsu ba a kansa.
Yakai dan uwana mai karatu idan ka lura zakaga cewa duk wdannan abubuwa akan hanya suke domin kuwa zai iya zama cikakkan hujjan lalace wan 'ya'yanmu ..
lailai wasu mutane sune ke auka 'ya'yansu cikin lalaci, alhali suna sane daga baya su dawo suna dana sani.
Akwai kuma mutanen da Allah kan jarabesu ne da mugun (da) misali Annabi Nuhu.ai dansa ba mai biyanya bane gashi kuma annabin Allah ne
Amma lailai duk mutumen da ya kyautatawa iyayensa ya bisu sau da kafa to shima idan Allah ya bashi 'ya'ya yan tarbiyya yan taddasu yan basu hakkinsu yan koya musu karatu da rubutu to,,,,kuma bai zalun cesu ba bai ciyadda su haram ba to Allah bazai kun ya tadda shi ba..
Musan man ka zaba musu uwa ta gari