Ala kulli halin, iyaye su za su sa ido ga 'ya'yansu maza da abokan da zasu dinga bi ko a makaranra ko gida.
Saboda yanzu zamani ya canza ,karamin yaro sai ka ganshi da mugayen kwayoyi na gusar da hankali.
kuma babban abinda ke kawo wannan shine halin ko inkula da iyaye maza keyiwa 'ya'yansu.
wani uban in ya fita,bazai dawo gida ba sai tsakan dare koma bawai sa na arsa ke sa shi hakaba,
to ku gayamin taya ya yaro in fita bazai lalace ba? sabo da a waje bashi da mai kula da tarbiyyansa, ko yana abinda ya sabama shari an musulunci babu mai kwabarsa.
ya zama dole musa karfi da karfe musawa yaranmu ido, don ganin sun tsira da cikekkiyar tarbiyya, domin duk ind kaga yara, to sune manyan gobe..
Don haka iyaye ya zama dole ku rinka ziyartar majalisar da 'ya'yanku suke zama, don ganin kuma kanku kun tsira da mutuncinku, a idon jama a kuma iyaye maza mune yan dace ku murinka sa ido ga diyanmu Maza, don mu ke fita waje, ba iyaye mataba a kuma dinga wa yara Maza fada don yawan sa kaya irin na kabilun kasan nan,
sai kaga matashi bashi da dogayen kaya, yana ganin su wai kauyanci ne a gareshi
To dan Allah iyaye muyi kokari iya bakin gwargwado agyara,
don yaron yanzu ka haife shine baka haifi halinsa ba
Zan dakata anan,
amma in sha Allah zamuyi tsokaci na gaba game da (MU SO AREWA)
sai mu dan tuna baya game da rawan da su Sardauna sunka taka a Arewa da kuma tarbiyyan da sunka bari mugani shin itace manmu na yanzu ke bi