Polly po-cket
HomeBlogAbout me
Nazif Yahya Megayya
MARABA DA ZUWA WANNAN SHAFIN MAI ALBARKA DAFATAN KAZO LAFIYA
2015-01-12
Zabi Inda Zaka Shiga Anan
Menu
Addinin Musulunci
Fassarar Usulus Sunnah
Labarai
Darika Shirka
Tambaya Da Amsa
Khudobin Malaman Sunnah
Salafiyya Network of Nigeria
Siyasar Nigeria
Yan Kasuwarmu
Hotona
Application
Games
.....................................................................
Wannan Shafin MallakarNAZIF YAHYA MEGAYYA
Ne
.......................................................................

Shafi Dan Karuwar Yan Uwa Musulmai

* No categories

Online: Guests: 1
Labarai

BAMBANCIN MU’UJIZA DA KARAMA Daga Umar Rabi’u Gwale 08091918143, 08022997576, 08152221688

BAMBANCIN MU’UJIZA DA KARAMA Daga Umar Rabi’u Gwale 08091918143, 08022997576, 08152221688
An dade ana yada jita-jita akan Ahlus-Sunnah da cewa (wai) bamu yarda da samuwar waliyyai da karamominsu ba, kuma abin mamaki mutane da yawa suna gaskata wannan sharri da qage na zunzurutun qarya zuqalaqe (Zuqi ta mallo). Tare da cewar, a qa’idar shari’a ba a saurin gaskata jita-jita, domin mafi yawan ta shiryayyiyar qarya ce ko kuma banqara gaskiya, ana cakuxa ta da qarya don cimma wani mugun nufi. Sai dai kuma yayin da mutum ya leqa littattafan Sunnah, da kuma sauraron karatun malaman Sunnah, to, kai tsaye zai gano tantangaryar rashin adalcin masu faxin waccar Magana, kuma zai fahimci Aqidar Ahlus-sunnah dangane da waliyyi ko karamar waliyyai, sai dai abin da suke kaucewa shi ne xaukar waliyyai a matsayin mutanen da suka san gaibu, ko marasa savo, ko kuma yi musu biyayya ido rufe. Tare da basu matsayin da bai kaucewa ma’aunin shari’a ba, wato Qur’ani da Hadisi bisa fahimtar magabata nagari. Ya xan’uwa ka sani cewa, wannan rubutu bai isa warware maka duk abin da ya shige maka duhu ba, dangane da sha’anin waliyyi, face dai xan tsokaci ne akan: BAMBANCIN MU’UJIZA DA KARAMA. To amma ka sani cewa waliyyan gaskiya sune, duk mumini (mai imani na gaskiya) da kuma tsoron Allah, kenan duk wanda ka ganshi ko ka ji yana savawa tafarkin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ko yana umarni da haka, to, wallahi ba waliyyi bane, xan duniya ne, mai tallan vaqar haja. To, bari in fara da ma’anar mu’ujiza da ta karama. Na Farko: Mece ce Mu’ujiza? A taqaice dukkan abin da wani Annabi ko Manzo, zai yi na ban mamaki, da keta al’ada cikin yardar Allah, ana kiransa mu’ujiza. Kuma ta kevanci Annabawa ne ko Manzanni (Alaihimus Salam), kamar raya matacce ga Annabi Isah (A.S.), lamarin san da ga Annabi Musa, tsagewar wata, zancen damo, da sauransu ga Annabin mu Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam). Na biyu: Mece ce Karama? A shar’ance in ance karama, ita ce wani lamari da ya savawa al-ada, wanda Allah yake gudanar dashi a hannun wani mutumin kirki, mai cikakken imani da tsoron Allah, wanda shi ba Annabi ko Manzo bane, don taimakonsa kan wani lamari na Addini ko na duniya. Kuma Ahlussunnah sun yarda da karamar waliyyai bisa ma’aunin Qur’ani da Sunnah. Duba Aqidatul Wasixiyyah. To, amma kafin mu duba bambancin Mu’ujiza da karama, bari kaji! Da yawan mutane an xorasu akan cewa, mutum ba zai zama waliyyi ba, sai ya riqe wasu wuridai da zikirai, ya yi su, ya shiga abin da suke kira HALWA, wato ya guji duniya, ya qauracewa mutane, ya zama yana kwana da yunwa, yana yawo kamar mahaukaci, cikin datti, wasu kuma za su yi tsaftar, to, amma wai sai mutum yafita daga mutuntakarsa, ya zama yana da siffofi irin na… kamar yadda mai Jawahiril ma’ani yake cewa “Haqiqanin waliyyi shi ne wanda ya fita daga siffar mutuntaka gaba xaya, sannan ya yi ado da halayen Ubangijintaka, zahiri da baxini (wal’iyazubillah)” Duba Jawahiril Ma’ani 2//66. Wannan fa misalin waliyyi kenan, a wajen, masu cewa, wai bamu yarda da samuwar waliyyi ba, to, in har da irin wannan ake zama waliyyi a mahangarsu, to, ai sune ma suke qaryata waliyyan gaskiya masu imani da tsoron Allah, waxanda basa aikata wani aiki face, sai ya dace da koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) babu daxi babu ragi. Na Uku: Bambancin Mu’ujiza Da Karama: Bari kaji malamin mu Malam Muhammad Rabi’u Umar R/Lemo, ya bambance mana tsakaninsu da faxinsa cewa “Karama tana da bambanci da mu’ujiza ta fuskoki da dama. Da farko dai ita kanta mu’ujiza, wato abin da Annabawa suke zuwa dashi, wanda ya savawa al’ada don tabbatar da Annabincinsa, ba ya zama gaskiya, ko ya nuna Annabcin wanda ya zo dashi, sai ta cika siffofi kamar haka: 1) Ya zama aikin da mai da’awar Annabta ya zo dashi, ba wanda zai iya yinsa sai Allah (Subhanahu Wata’ala). Da mutum zai yi da’awar Manzanci, ko ya ce shi Annabi ne, sannan ya ce mu’ujizarsa ita ce motsi da yake yi ko tsayuwa dayake yi ko zama ko tafiya, to ba ta zama mu’ujiza ba, saboda dukkan mutane ma zasu iya yin hakan. 2) Ta zama (mu’ujizar) ta savawa al’ada. Da mai da’awar Manzanci zai ce mu’ujiarsa ita ce, zuwan dare bayan rana, da hakan bai zama mu’ujiza ba. 3) Ya zama Mu’ujizar ta faru ne take lokacin da yake faxinta. 4) Kuma ta faru kamar yadda ya faxa, ba tare da ta savawa abin da ya faxa ba. Misali, da mai da’awar Annabci ko Manzanci zai ce, mu’ujizata ita ce, “Wannan dabbar ta yi magana” sai dabbar ta yi maganar, amma tace, “karya ka ke!” to, wannan ba mu’ujiza bace. Ci gaba zai zo a bugu na gaba insha Allah.
Back
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
.......................................................................


Ilmantarwa

Akhdari
Audio
Tauheed
Tarbiyya
Tafseer
Risala
Lugga
Kitabut Tauheed
Balagah
Fiqhu
Hausa Semenar
Karatukan Marigayi Sheik Auwal Albani Zaria AUDIO

Shiga nan dan sauke karatun malam akan illar polio
Shiga nan dan sauke karatun malam mai taken who taji tsoro Audio
Shiga nan dan Sauke karatun malam mai take who taji tsoro kashi na 2
Shiga nan dan Sauke karatun malam dayayi akan illar polio
Shiga nan Ka sauke lakcocin da malam yagabatar a lokacin rayuwarsa Audio
Shiga nan kasauke tafsir din da malam yagabatar 2013 Audio
Shiga nan kasauke karatun littafin KITABUL KABA'IR Audio
Shiga Nan ka sauke karatun littafin FIQHU SEERAH Audio
Shiga nan kasauke karatun FATWUL HAWAMIYYA Audio
Shiga nan kasauke karatul littafin TIBBU NABAWYY Audio
Shiga nan kasauke karatun littafin WATHEQATUL IKHWANI Audio
Shiga nan kasauke karatun littafin AHKAMUL EDI
Shiga nan kasauke karatun littafin SAHIHULMUSLIM Audio
Shiga nan dan sauke karatun littafin SIFFATUS SALATUN NABIYY Audio
Shiga nan dan sauke karatun littafin SARIMUL BATTAR Audio
Shiga nan dan sauke karatun littafin AQIDATUD DAHAWIYYA Audio
Shiga nan dan sauke karatun malam akan ASHURA
Shiga nan dan sauke Karatun littafin AHKAMUL EDII
........................................................................

Tafsir din Sheikh isah pantami

Shiga nan dan sauke karatun sheikh pantami Audio
........................................................................

Islamic Books

Qur'an in differance language
Ibni Kather
Sahihul Muslim
Sahihul bukhari,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Islamic Mujahidun

Hamas
Al-Aqida
Al-shabab
Islamic sites

Knaw more about islam
Meet with patner today
........................................................................

Bincike

Shiga nan domin duba dictionary na turanchi
Shiga nan dan translate na kalma
shiga nan dan new word 4 day
Shiga nan domin koyan turanchi
Shiga nan domin koyan karatu a layinka na mtn
Shiga nan domin tambaya da amsa a physic
Shiga nan dan koyan aikin jarida a BBC hausa
Shiga nan Dan koyan fasahar waya
Shiga nan dan koyan girki da hausa
Shiga nan da koyan karin magana da turanchi
.........................................................................

Dan Hausawanmu

Shiga nan dan samun labarai daga BBC hausa
Shiga nan dan karanta littafin MAGANA JARI littafi na 1
Shiga nan dan karanta littafin ILIYA DAN MAI KARFI na 1
Shiga nan dan karanta gajerun labarai
Shiga nan dan shiga shafin makaranta hausa
.........................................................................
Shiga nan dan karanta littafin RUWAN BAGAJA ........................................................................

Gyaran hoto da rubutu

Shiga nan domin sa hotonka a frame
Shiga nan domin hada ID CARD
shiga nan karubuta abinda kake so sannaaan kasauke a wayarka
Shiga nan domin sanya hotonka a frame sannan ka sauke a wayarka.........................................................................

Bincike a Internet
Shiga nan dan engine dinmu domin seach din abinda kake so
shiga nan domin yin seach a google
shiga nan domin seach a yahoo
shiga nan domin yin seach a wikipedia
shiga nan domin yin seach a tubidy
.........................................................................

Social Network Issues

Shiga dan sanin yadda ake bude facebook
shiga nan dan canza passwrd dinka na facebook 2
shiga nan dan sanin yadda ake canza password din facebook
Shiga nan domin sanin yadda zaka canza sunanka na facebook
Shiga nan dan canza Email dinka na facebook
Shiga nan dan sanin yadda ake bude twitter
shiga nan dan canza password dinka na twitter
Shiga nan dan sanin yadda ake bude eskimi chat
shiga nan dan sanin yadda ake canza password na eskim
.........................................................................

Yadda Ake Bude Email

shiga nan domin koyan yadda ake bude Emai
shiga nan dan koyan yadda ake bude yahoo
shiga nan dan sanin yadda ake bude hotmail
.......................................................................

Yadda Ake Bude Website/blog

Shiga nan dan ka bude irin wannan shafin
Shiga nan dan bude website
Shiga nan dan bude waplog siteShiga nan domin bude word press
Shiga nan dan bude over blog site
Ga duk wanda bai iya budewa da kansa to ya tuntube ni insha Allah za'a bude mai batare da bata lokaciba
........................................................................

Hada Logo
Shiga nan dan hada logo daga hausa wap
Shiga nan dan cool text domin hada loga
Shiga nan dan text space domin hada logo
Shiga nan dan hada logo
shiga nan dan hada freelog service
Shiga nan dan hada logo a disignmentic
Allahumma Salli Wasallim Ala Nabiyyina Muhammad.........................................................................
.........................................................................

Shafuka Masu Alaka Damu

Jibwis Nigeria
Darus Sahaba
Shafin Basheer jounalist sharfadi
Shafin Sunnah sak
Shafin El-hussaini sulaiman megayya
shafin m. Anas Assalafiyy
Shafin Taskar sunnah
........................................................................

Cooltext18ny Megayya
Ra'ayin Jama'a Game Damu
3.........................................................................
Kubiyoni ta account dina na facebbo ta nam
........................................................................
Click to Call
Click to Sms
.........................................................................
Ahlusunnaj
Kubiyo ni ta babban shafin mu na facebook ta nan
Ko kuma ku biyomu ta babban dandalinmu na facebook tanan
.........................................................................

2015-01-12