Anyi Kira ga Jama'a da su baiwa 'yan Agaji Hadin kai a lokacin bincike yayi gabatar da Sallar Juma'a
Injiniya Salisu Muhammad Gombe, Shine Shugaban kungiyar izala ta jihar Gombe, kuma Sakataren Shirye Shirye a Majalisar agaji ta kasa, shi yayi wannan kira yayin gabatar da Sallar Juma'a a masallacin Bolari dake garin Gombe a yau juma'a.
Shugaban ya bada Umurni ga yan Agaji da su chaje kowa kafin shiga harabar Masallacin, inda aka fara da chaje shugaban kamar yadda kuke gani a hoto kafin ya shiga cikin masallacin domin samun kyakkyawan tsaro a lokacin gabatar da ibada.
"Muna kira da babbar Murya ga Jama'a da su baiwa yan agaji hadin kai a lokacin gabatar da duk wasu tarurrika na addini, ta wannan hanyar ne kawai zamu cimma burin mu na zakulo masu kashe mutane a wuraren ibada, muyi hakuri da duk wani binciken da za'a mana domin mu gudu tare mu tsira tare". Inji Shi"
Daga karshe muna godiya ga Al'umma kan kokari da hakurin da sukeyi da yan agajin mu a lokacin gabatar da aiki, muna addu'an Allah ya kawo mana karshe wannan tashin tashina da ya addabi al'ummar musulmi a wannan kasa tamu ta Nijeriya. Amin.
UNDER MAINTENANCE