80s toys - Atari. I still have
HomeBlogAbout me
Nazif Yahya Megayya

TARIHIN SHEIKH YAKUBU MUSA SAUTUS SUNNAH

Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina. (Sautussunnah).

An Haifi Malam a Shekarar 1947 a cikin Garin Gwaram Jihar Jigawa, kuma Yafara Karatu Tun Yana Yaro a Hannun Wani Sanannen Malami kuma Kawunsa Malam Mahmoud a garin kano, Malam Ya Haddace Qur'ani tun Yaro, Daga Bisani Yacigaba Da Karatun Litattafai (Fiqhu,Tauhidi da Tarihi) Daganan Yakoma Garin Jos, wurin dan uwansa, wani Malamin Mai suna Sheikh Ibrahim Mushaddadu inda Daganan Yacigaba Da Karatun Primary a makarantar Jama'atu anwaril hudaya wanda ke karkashin Nasirul Islam, Malam Ya koyi Litattafai da Dama a Jos.

Kafin Daga Bisani Kungiyar Nasrul Islam a shekarar 1973 Karkashin Jagorancin Shugabanta na tsohuwar jihar Benue da plateau, Alkalin Alkalai Alhaji Ahmadu Arabi Ya Tura Malam a Matsayin mai wa'azi Garin Kafanchan Domin wa'azi Da Koyarwa. Yakuma Yi Amfani da wannan Damar Yayi ta wa'azi yakuma Kafa Makarantar (Mikratul Islam School) ya Horar Da Matasa Da Dama cikin Shekaru Shida Malam Yasamu Nasarori Dayawa.

Kafin Daga Bisani wasu daga cikin Matasan Malaman Addinin musulunci Masu wa'azi Sukayi Yunkurin Kafa Wata kungiyar Wa'azi mai Suna Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa Iqamatis Sunnah, domin Kawar da Bidi'a da Kafa Sunna, Malam Yakubu Musa Yana Cikin wadanda Suka Kafata Tare da Su Marigayi Sheikh isma'ila idris Bin Zakariyya Jos, wanda shine Shugaban Majalisar Malamai a wancan lokacin, Malam Yakubu Musa Mataimakinsa.

Daga Bisani Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Yakira Malam Yakubu Musa Yaturashi Katsina Makarantar zurfafa karatun addinin Musulunci Da koyon wa'azi, Mai Suna Arabic Teachers Collage (ATC) inda Yazama Dalibi Dayayi fice acikin Dalibai Bayan Daya Kammala,Yashiga Makarantar Kimiyya Da Fasaha Ta Katsina (polytechnic) inda ya karanta shari'ar musulunci da na zamani, Ananma Yazama Dalibin Dayafi Kowanne Dalibi Hazaqa Bayan Kammala Karatunsa Ya cigaba Da Kafa Makarantu Yana Koyar Da matasa Da Matan Aure Har Yayi Nasarar Kafa Makarantar "Musbahuddeen Islamic School" Yakuma sake Kafa Makaranta ta Farko Da'ake Karatun Addini dana Zamani. (Riyadhul Qur'an Islamic School) Tasamu Dalibai Masu Hazaqa daga kowanne Bangare na Kasarnan dama kasashen yammacin africa. Makarantar tafi bada Karfi a Bangaren Qur'an da Hukunce Hukuncen Karatu da Tauhidi, Wanda har zuwa yau dinnan ana karatu a makarantar, Kuma Mallam ya kafa Makarantun Sautus Sunnah international comprehensive schools inda ta hada bangarorin ilimin addini da na zamani da kuma bangaren da'awah ta mata.

Wannan Na Daga cikin Irin cigaban Da Sheikh Yakubu Musa Yakai Jihar Katsina da kasa baki daya.

A karshe, mallam ya rike mukamai Kamar haka :

1. National Chairman Da'awa Commitee Jibwis Nigeria
2. Member Board Of Trustees Jibwis Nigeria
3. Member National Exco JIbwis Nigeria
4. Member Council of Ulama Jibwis Nigera.
5. Member National Shura (The Highest decision council)SCSN
6. Katsina State Chairman Jibwis Nigeria.
7. Katsina State Chairman Supreme Council For Shari’a in Nigeria
8. Member in Zamfara state Council of ULAMA
9. Member Jigawa State Council of ULAMA

Wasu Mukaman Har Yanzu Malam Shi Yake Jagorantar su bai gajiya ba.

Da kuma wasu kwamitoci daban daban, kuma malam Dattijo ne cikin Dattawan kungiyoyi da majalisu daban daban na harkokin addini.

Malam yana da kokarin fadin gaskiya gaban ko wanene, haka zalika Malam yakan tsaya tsayuwar mai daka a duk lokacin da ya fahimci akan gaskiya yake, ta wannan dalilin Malam ya shiga kurkuku ba adadi, kuma bai sauka daga inda aka sanshi ba tun farko na kekashewa akan gaskiya.

Mallam ya samu Nasarorin amsan kyaututtukan yabo kala daban daban daga hukumomi da kungiyoyi, kuma ya samu nasaran zama daya daga cikin Jaruman Jihar Katsina da kuma littafi da ake bugawa na (The Great Heroes of Katsina) .kuma yana cikin (500 The world’s most influencial muslims)
Kuma Allah ya azurta Mallam da yara 25 da jikoki sama da 53. Cikin 'ya'yan Malam yana da magada da yawa irin su Sheikh Muhammad Aminu Yakubu Musa wanda yayi karatun Digirinsa a jami'ar Musulunci ta kasar Suda, da Sheikh Saifuddeen Yakubu Musa wanda a yanzu yake karatun Digirinsa na biyu a jami'ar Musulunci

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE