XtGem Forum catalog
HomeBlogAbout me
Nazif Yahya Megayya

HUKUNCIN KARBAR KYAUTAT KIRSIMATI

HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRSIMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA'LIH SUKA YI BAYANI

1- Da yake Alhamis mai zuwa ne Kiristoci za su fara abin da suke kira bukin kirsimeti (idin kirsimeti) wanda suke yin shi ko dai a ranar 25/12 M ko kuwa a ranar 7/1 M.
2- Sannan da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin su Kiristoci da kuma al'ummar Musulmi.
3- Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai.
4- Sannan da yake akwai masu bidi'ah da dama da ke halatta abin da Shari'ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari'ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al'ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al'ummar Musulmi.
**************************
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-

Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da bata da kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta -kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi'ar idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ce kuwa a shekarar miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.

Na biyu: Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih -Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'uttaabi'in- dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqii ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
((اجتنبوا أعداء الله في عيدهم)). انتهى.
Ma'ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)). Intaha.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-
((وليس للمسلمين ان يعينوهم على أعيادهم لا ببيع ما يستعينون به على عيدهم ولا باجارة دوابهم ليركبوها في عيدهم لان أعيادهم مما حرمه الله تعالى ورسوله صلى الله عليه وسلم لما فيها من الكفر والفسوق والعصيان)). انتهى.
Ma'ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)). Intaha.

Na uku: Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-

Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan bangarorin Kiristoci ke bi.

Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da bangarorin Orthodox ke bi.

Na hudu: Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas'ala cikin shari'ar Musulunci.

Na biyar: Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da Kiristoci, su wannan nau'i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da kuma auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka.
*************************
Idan Musulmi sun fahimci wannan sai mu shiga bayanin mas'alarmu da muke son yi wa jama'a bayaninta, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ta

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE