A Najeriya yanzu haka an soma amfani da sabuwar takardar kudi ta Naira 100 a hukumance wadda gwamnatin Nijeriyar ta bullo da ita

Hukumomin kasar dai sun ce za a ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 100 da kuma sabuwar da aka samar a lokaci guda.
An kirkiro da sabuwar takardar kudin ta Naira 100 domin tunawa da cikar kasar shekaru 100 da kafuwa.
Hakazalika shigowar sabuwar takardar kudin na zuwa ne a daidai lokacin da darajar kudin Nigeriar ke ci gaba da faduwa sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya.
Created at 2014-12-19 21:36
Back to posts
UNDER MAINTENANCE