HomeBlogAbout me
Nazif Yahya Megayya

AN UMARCHI JAMA'A DASU BAIWA YAN AGAJI GOYAN BAYA YAYI SHIGA MASSALLACI

AN UMARCHI JAMA'A DASU BAIWA YAN AGAJI GOYAN BAYA YAYI SHIGA MASSALLACI
An Umurci 'yan Agaji da su binciki kowa yayin shiga Masallaci ko wani wurin taron jama'a yayin gabatar da tarukan addini. Umurinin ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, inda ya bukaci jagirorin addini da mabiya da su baiwa yan agaji hadin kai domin tantace masu shiga masallacin, Lura da yadda yanayin kasar ya chanja tare da kokari wurin inganta tsaro a lokacin gabatar da ko wace irin ibada. Shehin Malamin ya kara da kiran yan agajin da su kara inganta tsaro a masallatan mu na khamsul salawat, makaranti da sauran wuraren hada hadar jama'a na tarukan addini. Sheikh Bala Lau ya bada Umurni ga yan Agaji da su chaje kowa kafin shiga harabar Masallaci, a duk fadin kasar, inda aka fara da chaje shugaban kamar yadda kuke gani a hoto kafin ya shiga cikin masallacin domin samun kyakkyawan tsaro a lokacin gabatar da ibada. "Muna kira da babbar Murya ga Jama'a da su baiwa yan agaji hadin kai a lokacin gabatar da duk wasu Tarurruka na addini, ta wannan hanyar ne kawai zamu cimma burin mu na zakulo masu kashe mutane a wuraren ibada, muyi hakuri da duk wani binciken da za'a mana domin mu gudu tare mu tsira tare". Inji Shi" Daga karshe muna godiya ga Al'umma kan kokari da hakurin da sukeyi da yan agajin mu a lokacin gabatar da aiki, muna addu'an Allah ya kawo mana karshe wannan tashin tashina da ya addabi al'ummar musulmi a wannan kasa tamu ta Nijeriya. Amin.
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE

Teya Salat