Old school Easter eggs.
HomeBlogAbout me
Nazif Yahya Megayya

SUWAYE SUKE ZIKIRIN GASKIYA TSAKANIN YAN BIDI,A DA AHLUSSUNA

SUWAYE NE SUKE HAKIKANIN ZIKIRIN DA YA ZO DAGA QUR'ANI DA SUNNAH, TSAKANIN AHLUSSUNNAH DA AHLUL BIDI'AH???


Sau da dama zakaga cewa 'yan Bidi'ah suna tuhumar Ahlussunnah da cewa Ahlussunnah sun hana ayi zikiri ko kuma kwata-kwatama suce Ahlusuunnah basa yin zikiri. Ya kamata mu danyi bayani a takaice domin mu kare kanmu daga wannan zargin da 'yan Bidi'ah ke yi mana.

ยค FALALAR ZIKIRI.

Aya ta farko, Allah madaukakin sarki ya ce: ( "Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" (Suratul Bakara, aya ta 152) Wannan ayar tana karantar da mu cewa idan muka ambaci Allah (zikiri), to Allah ma zai ambace mu sannan mu gode masa kada mu kasance batulallu.

Aya ta 2. "Yaa ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa" ( Suratul Ahzab, aya ta 41) Wannan ayar tana umurtan dukkanin wani mai imani da cewa su amci Allah ambato mai yawa, ma'ana kuyi zikiri zikiri mai yawa. Sannan kuma abin lura anan shine, ba fa umurni ne ga duk wani musulmi ba, a'a umurni ne da ya takaita ga masu imani.

Aya ta 3. "Da masu ambaton Allah (zikiri) da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu da gafara da lada mai girma" (Suratul Ahzab, aya ta 35) Kai!!!


Ashe zikiri babban abune domin kuwa wannan ayar da bada garabasa da rahusa ga masu yin zikiri.

Domin kuwa Allah ya tanadar musu da gafara sannan bayan gafarar; Allah zai kara musu da lada, sannan ladanma sai Allah yace "Aziima" Ma'ana lada mai yawa. Ashe zikiri babban abu ne, to amma ya Allah ya ce ayi zikiri???


Sai mu koma suratul A'araf inda Allah madaukakin sarki yake cewa: "Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kaskan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (Tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu" (Suratul A'araf, aya ta 205).

Wannan ayar tace ka ambaci Ubangijinka ma'ana kayi zikiri a cikin zuciyarka.

Idan mutum zaiyi zikiri a cikin zuciyarsa baya bukatar ihu da sowa da firgicewa.

Sannan sai Allah ya ce kuma a yayin zikirin ka kasance mai kaskan da kai da tsoro a gare shi.

Idan ance kankan da kai, ashe kuwa ba za'a sa shauki a cikin zikirin ballentana har a sa ganga da jita da kalangu ko kuma Piano.

Kuma Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ya ce (Misalin wanda ya ke ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayye ne da matacce) Sannan Annabi yace (Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakanku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gareku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku?

Suka ce ka ba mu labari Yaa Rasulullah.

Sai yace: Ambaton Allah madaukaki) Daga Abbdullahi Ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: ya Ma'aikin! Shari'o'in musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: (Kar harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton Allah SWT). Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya ce (Wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah.

Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba, shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah).

Abin suna da yawa, amma bara in takaita anan.

Duk abinda zakayi, to akwai zikirin da annabi ya karantar matukar dai abin a addini ne ba a cikin hidimomin ra'ayuwa ta duniya ba.

Saboda haka ashe mu Ahlussunnah ba wai muna kin zikiri ba ne.

Mu abinda mukace ayi zikirin yanda Allah da MansonSa (s.a.w) suka karantar da mu! Kuma hakan mai sauki ne domin akwaisu a rubuce a littatafan Addini.

Duk abinda babu Nassi a kansa sannan aka jinginawa Musulunci da wannan abin to ya tabbata a yayi Bidi'ah.

Itama kuma Bidi'ah tana cinye ayyukan bawa inji Annabi Muhammad (s.a.w) sannan a hadisin da aka karbo daga wajen Aisha Uwar Muminai (RA) ta ce taji Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Duk wanda ya kago wani abunda babu shi a cikin lamarinmu (Na Addini) to an mayar masa) Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Sannan Annabi Muhammad (s.aw) yana tsoratat da mu da yin Bidi'ah a cikin addini kamar yanda yazo a hadisin Abi Najihin al-Irbabu dan Sariyatu (RA) wanda Abu-Dauda da Tirmidhiy suka ruwaito, inda karshen hadisin yake cewa:

Yaa Allah ka gafarta mana kurakuren mu.

Zan samu lokaci in dan kawo zikirorin da suka tabbata daga Annabi Muhammad (s.a.w) ba irin wanda yan Bidi'ah suke wahalas da kansu a kai ba. "

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE